Shugaban wanda ya yi wannan kira a jiya Lahadi, a yayin taron karawa juna sani karo na 38, wanda hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS ta shirya, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sauye sauye, ga tsarin tattalin arzikin kasar.
Ya ce ya zama wajibi kasar Sin ta yi amfani da wannan dabara, ta daidaita tsarinta a fannin masana'antu da harkar samar da kayayyaki, kuma matakin farko shi ne samar da hajoji masu inganci, da hidimomi masu nagarta a tsarin tattalin arzikin kasar, matakan da daga karshe, za su haifar da ci gaba mai dorewa wanda kasar ke fata.
Har wa yau shugaba Xi, ya ce manyan matsalolin da ke yiwa tattalin arzikin kasar Sin tarnaki a yanzu haka, ba su wuce na tsare tsare ba, wadanda kuma suka shafi fannin samar da kaya da na cinikayyar su, musamman ma fannin samar da hajojin.
Daya daga fitattun masana a hukumar wanzar da ci gaba, da gudanar da sauye sauye ta kasar Sin Chen Dongqi, ya gabatar da makala game da wannan jigo, yayin taron na karawa juna sani.(Saminu Alhassan)