Babban bankin kasar Sin ya bayyana cewa, kudaden ajiyar ketare na kasar ya ragu a karo na bakwai a jere a watan Janairun zuwa dala tiriliyan 3.
Hukumar kula da kudaden ajiyar ketare ta majalisar gudanarwar kasar Sin(SAFE) ta bayyana cewa, a watan da ya gabata kudaden ajiyar ketare na kasar ya kai kimanin dala tiriliyan 2.99, kana ya ragu zuwa dala tiriliyan 3.01 a watan Disamba.
Hukumar SAFE ta danganta wannan koma baya kan matakan ceto asusun ajiyar ketare na kasar daga halin da kasuwa ta shiga.
Sai dai kuma majalisar gudanarwar ta bayyana cewa, dama kudaden ajiyar ketare sun gaji karuwa da raguwa, idan aka yi la'akari da yanayin tattalin arzikin da ake fuska a gida da kuma kasashen katare.
Haka kuma duk da koma baya da harkar hannayen jari ta fuskanta, ana hasashen cewa za ta kankama a nan gaba.(Ibrahim)