Rahoton ya kuma bayyana cewa, yadda kasar Sin ta sauya tsarin tattalin arzikinta domin kara inganta bukatun al'ummomin kasar zai tallafawa sauran kasashen duniya, ko da yake, nan gaba kadan, lamarin zai kasance kalubale ne ga tattalin arzikin duniya, amma, idan aka kalli batun ta bangaren dogon lokaci, mai yiwuwa, zai samar da dammamaki masu kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Bugu da kari, wani masanin ilmin tattalin arziki a sashen nazari na asusun IMF ya bayyana a yayin taron gabatar da rahoton da aka yi cewa, wajibi ne kasar Sin ta sauya tsarin tattalin arzikinta, da zummar tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arzikinta, har ma da kasashen duniya baki daya.
Haka kuma, masanin ya ba da wasu shawarwari ga wasu kasashen da watakila sauyin tsarin tattalin arzikin kasar Sin zai iya yi musu tasiri, inda ya ce, ya kamata a daidaita dangantakar cinikayya dake tsakaninsu da kasar Sin yadda ya kamata, ya fi kyau su kyautata tsarin bunkasuwar tattalin arzikinsu bisa manufofi na siyasa. (Maryam)