Wadannan kasashe su kuma kasance babban ginshikin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya, musammam ma kasar Sin wadda ta ba da babbar gudummawar a zo a gani a wannan fanni.
Haka zalika, madam Lagarde ta bayyana a yayin da ta halarci wani bikin da kwalejin nazarin kasuwanci ta Kellogg ta jami'ar Northwestern dake kasar ta Amurka ta shirya a ran 28 ga wata cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da bunkasa cikin sauri, a yayin da kasar ke sauya tsarin tattalin arzikinta.
Bugu da kari, ta jaddada muhimmancin yaki da nuna kariyar cinikayya, inda ta yi kira ga kasashen duniya, da su fara aiwatar da sauye-sauye a tsarin tattalin arzikinsu bisa la'akari da halin da suke ciki, yayin da ake daidaita manufofi a tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samu ci gaban tattalin arziki a duniya baki daya. (Maryam)