An samu fashewar boma bomai ne a wata tashar man fetur na wani garin dake gabashin birnin Hilla. Inda wata mota mai cike da boma bomai ta fashe a wani yankin da aka kebe cikin tashar man fetur din domin jiran zuba mai cikin mota. Kasancewar akwai manyan motoci masu dauke da fasinjoji a kewayen motar a lokacin da lamarin ya faru, shi ya sa harin ya haddasa mutuwar mutane masu dimbin yawa.
Bayan abkuwar harin, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta sanar da daukar alhakin kai harin.(Fatima)