in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan IS 97 yayin hare hare da Amurka ke jagoranta a Iraqi
2016-12-26 09:58:03 cri
Rahotanni na cewa a kalla mayakan kungiyar IS 97 ne suka rasa rayukansu, yayin samame da dakarun sojojin hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta suka kaddamar, a sassan birnin Mosul dake arewacin kasar Iraqi.

Wata sanarwa da dakarun hadin gwiwar na Iraqi suka fitar ta bayyana cewa, mayakan kungiyar ta IS sun yi arangama da dakarun sojin hadin gwiwar ne a ranar Lahadi, bayan da mayakan na IS suka yi yunkurin kaddamar da wasu hare haren kunar bakin wake a yankunan Al-Intisar, al-Shaima, da Al-Salam dake kudu maso gabashin birnin na Mosul, lamarin da ya sabbaba kisan mayakan na IS su 51.

Kaza lika dakarun hadin gwiwar sun kuma lalata wasu motocin da IS din ta yi yunkurin amfani da su, wajen kaddamar da hare haren bama bamai.

A yayin wata arangamar da ta auku a kudancin birnin na Mosul, dakarun gwamnatin kasar sun hallaka mayakan IS 21, tare da lalata motoci 2 na kunar bakin wake. Kaza lika bisa wasu bayanan sirri da dakarun gwamnatin suka samu, an kaddamar da wasu hare hare ta sama kan wani ginin dake unguwar al-Wahda, ginin da a cikinsa ake kyautata zaton wasu mayakan IS din ke shirya yadda za su kaddamar da hari kan dakarun tsaro.

An dai ce wannan matakin soja shi ma ya sabbaba kisan mayakan na IS 25.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD dai ta fidda wani rahoto dake nuna cewa, kimanin mutum 103,872 da suka kunshi maza da mata da yara kanana ne suka tsere daga birnin Mosul, da ma sauran garuruwan dake makwaftaka da shi, tun bayan fara daukar matakan soji a yankin a farkon watan Oktobar bana, a wani mataki na kwace yankin wanda shi ne tungar mayakan na IS a kasar Iraq. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China