Firaministan kasar Iraqi Haider al-Abadi, a jiya Talata ya ayyana kwato bangaren gabashin birnin Mosul bayan shafe sama da watanni uku ana gwabza kazamin fada da mayakan kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci.
Haka zalika, Abadi, ya bukaci jami'an wanzar da tsaro da su hanzarta komawa ragowar yankunan da suka rage domin kwato su baki daya, wadanda suka hada da lardin Nineveh dake arewacin Iraqi, musamman yammacin birnin Mosul, wanda aka fi sani da yankin tekun Tigris, wanda aka balle shi daga birnin.
Firaministan yayi wannan kiran ne a yayin taron manema labarai, inda ya yabawa dakarun sojojin hadin gwiwa na Iraqi.
Bugu da kari, wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce, sojojin Iraqin sun yi nasarar kwato gabashin Mosul ne bayan sun kwace ikon dukkannin yankunan da suka rage a hannun mayakan na IS dake wajen arewacin birnin gabar teku na gabashin birnin.(Ahmad Fagam)