in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin tattalin arziki da cinikayya na kasashen BRICS sun cimma matsaya daya a fannoni daban daban
2016-10-16 13:23:19 cri
A jiya Asabar 15 ga wata, shugaban sashen kula da harkokin hulda da kasa da kasa ta ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, Zhang Shaogang ya bayyana cewa, ministocin tattalin arziki da cinikayya na kasashen BRICS sun riga sun share fagen gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS karo na 8, bangarori daban daban sun amince da ci gaba da tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Hangzhou na kungiyar G20, da karfafa hadin gwiwar kasashen BRICS a kungiyar WTO da G20 da sauransu, da nuna goyon baya ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da kuma yaki da kariyar cinikayya, da zummar kiyaye yanayi mai kyau na tattalin arziki da cinikayya a duniya.

A yayin da yake gabatar da yanayin da ake ciki ga kafofin yada labarai na kasar Sin, Zhang Shaogang ya bayyana cewa, an gudanar da taron ministocin tattalin arziki da cinikayya na kasashen BRICS a karo na 6 a ranar 13 ga wata a birnin New Delhi. A matsayin muhimmin taron share fagen taron shugabannin kasashen BRICS a birnin Goa, mahalarta taron sun cimma matsaya daya a fannin tattalin arziki da cinikayya, hakan ya samar da babban kuzari a fannin siyasa ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS a wadannan fannoni.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China