in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta fi mai da hankali kan fannoni 4 game da kungiyar BRICS
2017-01-03 20:16:41 cri
A yayin wani taron manema labaru da aka saba shiryawa yau Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Geng Shuang, ya bayyana cewa, a lokacin da kasar Sin take shugabantar kungiyar BRICS, za ta fi mai da hankali kan fannoni hudu.

Mr. Geng ya ce da farko dai, Sin za ta fi mai da hankali kan yin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, sannan za ta kara mai da hankali kan gudanar da hadin gwiwa a sauran fannonin cinikayya da zuba jari, da yin musayar kudade, gami da ayyukan yau da kullum a fannin, da kuma yin musayar mutane da al'adunsu.

Bugu da kari, za ta fi mai da hankali kan yadda kasashe mambobin kungiyar BRICS za su iya daidaita matakansu kan wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin kyautata hanyoyin tafiyar da harkokin kasa da kasa, da shawo kan kalubalen da ake fuskanta a duk fadin duniya. Sannan Sin din za ta kara mai da hankali wajen yin musayar mutane da al'adunsu, ta yadda al'ummomin kasashen kungiyar BRICS za su kara sanin yadda kasashen ke yin hadin gwiwa, da haifar musu da alherai. Daga karshe, kasar Sin za ta kara yin kokari wajen kyautata manufofin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, domin shigar da karin abokai a cikin kungiyar. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China