Gungun kasashen da tattalin arzikin da ke samun bunkasuwa na BRICS dake kunshe da kasashen Brazil, Sin, Indiya, Rasha da Afrika ta Kudu, sun fitar a ranar Lahadi da wata sanarwar hadin gwiwa bayan wani zaman taro na shugabannninsu a Goa, inda suka dauki niyyar taka muhimmiyar rawa da kara taimakawa ga tsare tsaren na tafiyar da harkokin duniya.
Sanarwar Goa ita ce sakamako na dandalin BRICS karo na 8, da ya gudana a ranakun 15 da 16 ga watan Oktoba a jihar Goa dake yammacin Indiya, bisa taken " Gina hanyoyin da suka dace, daga dukkan fannoni da bisa halartar kowa'.
Sin, za ta karbi shugabancin gungun kasashen BRICS a shekara mai zuwa, kuma za ta barbi bakuncin taron shekara shekara na gungun a cikin watan Satumba, a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin Sin, in ji shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Lahadi.
Sin na hasashen yin aiki tukuru tare da dukkan bangarori daban daban da abin ya shafa domin aiwatar da matakan da aka tsara a yayin manyan tarukan da suka gabata, domin zurfafa dangantaka a cikin mambobin gungun BRICS, da kuma rubuta wani sabon babi a cikin dangantaka tsakanin kasashen BRICS, in ji mista Xi a yayin taron kasashen BRICS karo na 8 a jihar Goa dake yammacin Indiya. (Maman Ada)