Shugaba Xi, ya yi wannan kira ne a sakon da ya aikewa shugaban Rasha Vladimir Putin, da shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma, da shugaban Brazil Michel Temer, da kuma firaministan Indiya Narendra Modi, inda ya gabatar musu da takaitaccen bayani game da cikakken shirin kasar Sin kan yadda za'a bunkasa hadin gwiwar kasashen BRICS a shekarar nan ta 2017.
Shugaban ya ce, kasar Sin ne za ta karbi bakuncin taron kolin na BRICS karo na 9 a Xiamen, wani muhimmin birnin dake kudu maso gabashin kasar Sin a lardin Fujian a watan Satumba. (Ahmad Fagam)