A yayin taron, shugabanni biyar na kasashen BRICS da shugabannin kasashen Sri Lanka, Bangladesh, Bhutan da Nepal da dai sauransu, da kuma babbar ministan Myanmar, wakilan gwamnatin kasar Thailand sun yi shawarwari kan yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da kasashe masu tasowa.
Haka kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS da bangarori daban daban zuwa wani sabon matsayi, ta hanyar yin amfani da dandalin tsarin BRICS da kuma bisa ka'idojin nuna fahimtar juna da cimma moriyar juna. (Maryam)