Jaridar ta ce, an fara gabatar da shawarar kafa hukumar ce a wajen wani taron shugabannin kungiyar BRICS da ya gudana a shekarar 2015, daga bisani aka sake tabbatar da wannan aniyyar a cikin sanarwar da kungiyar ta bayar a Goa na kasar Indiya. A halin yanzu, kungiyar ta sa wasu masanan ilimin hada-hadar kudi da su yi nazari game da dabarun da za a dauka don kafa wannan hukuma.
Bayanai na nuna cewa, ana son kafa wannan hukuma ce domin wasu manyan hukumomin da ke auna karfin tattalin arziki 3 da suka shahara a duniya, wato Standard & Poor, Moody's, da kuma FTICH, dukkan su suna aiki da manufofin da kasashe masu sukuni suka tsara ne. Saboda haka, akwai rashin adalci, yayin da ake auna karfin yanayin tattalin arziki a kasashe masu tasowa, gami da kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa, lamarin da ya sanya kasashe da yawa yin korafi a kansa.(Bello Wang)