A wannan rana ne kuma wakilin musamman na MDD dake kula da batun Syria Staffan de Mistura, ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, zai gana da tawagar wakilan gwamnatin kasar ta Syria, da tawagar wakilan masu adawa a daren ranar jiya Alhamis da kuma Jumma'ar nan, domin tattaunawa da kuma cimma matsaya, kan jadawalin shawarwarin wannan zagaye, da kuma yadda za a gudanar da shawarwarin tsakanin sassa daban daban, ta yadda za a gaggauta yanke matsaya kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi zaman.
Bugu da kari, ya ce, an tsara babban taken shawarwarin nema sulhu na wannan zagaye bisa kudurin MDD mai lambar 2254, inda za a mai da hankali kan harkokin dake shafar kafuwar gwamnatin wucin gadi, da tsara sabon kundin mulkin kasa, da kuma yadda za a sake gudanar da babban zabe a kasar.
A daren wannan rana kuma, Mr. Mistura ya shirya liyafar maraba da zuwan wakilan sassan biyu, a fadar "palace of nations" dake birnin Geneva. Kuma wannan shi ne karo na farko da wakilan gwamnati da wakilan 'yan adawar kasar ta Syria, suka halarci wani biki gaba da gaba a birnin na Geneva.
Sai dai ya zuwa yanzu, ba a san ko sassan biyu za su yi shawarwari kai tsaye ba, yayin zaman tattaunawar sulhun da za a yi, cikin kwanaki da dama mai zuwa. (Maryam)