Sanarwar ta bayyana cewa, an riga an mika takardun gayyata ga wakilai mahalarta a ranar 13 ga wata, kana ana kokarin share fagen taron. An ce, wakilai mahalarta za su isa birnin Geneva a ranar 20 ga wannan wata don tattaunawa tare da Mistura da tawagarsa kafin bude shawarwarin a ranar 23 ga wata.
Ya zuwa yanzu, an riga an jinkirta lokacin sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a Syria sau biyu, Mistura ya taba sanar da gudanar da shawarwari a ranar 8 ga wannan wata, amma ya bayyana cewa an dage zaman sai zuwa ranar 20 ga watan nan da muke ciki.
A farkon shekarar 2016 ne, wakilan gwamnatin kasar Syria da kungiyar masu adawa ta kasar sun yi shawarwari sau da dama a birnin Geneva, amma ba su cimma daidaito ba. Bisa shiga-tsakani da Rasha da Turkiya da Iran suka yi, an yi shawarwarin kula da batun Syria a birnin Astana na kasar Kazakstan a watan Janairu na shekarar nan ta 2017, wanda ya aza tubalin sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Syria. (Zainab)