in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Jordan da Lebanon sun nanata goyon bayansu ga kokarin ganin an tsagaita bude wuta a Syria
2017-02-15 10:56:48 cri

Kasashen Jordan da Lebanon sun sake nanata bukatar ganin kasashen duniya sun kara kokarin da suke na ganin shirin tsagaita bude wuta a kasar Syria ya kankama.

Sarki Abdullah na II na kasar Jordan da shugaba Michel Aoun na Lebanon ne suka bayyana hakan yayin wata ganawa a birnin Amman. Suna masu bayyana muhimmancin tsugunar da 'yan gudun hijirar kasar Syria a kasashen biyu.

Bugu da kari, shugabannin biyu sun jaddada bukatar daura damarar yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a matakan yankunan da kuma kasa da kasa. A saboda haka, suka kara yin kira ga kasashen Larabawa, da su kara daukar makatan da suka wajaba na ganin an magance abubuwan dake kawowa kasashen Labarawa matsala.

Shugabannin sun kuma kara nanata muhimmancin taron kolin kawancen kasashen Larabawa da ke tafe, da bukatar hade matakan da kasashen Larabawan suke dauka tare da karfafa hadin gwiwa kan yadda za a magance tarin kalubalen da ke damunsu baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China