Birnin na Al-Bab dai na da iyaka da kasar Turkiyya, kuma ya fada hannun dakarun sojin Turkiyya, da hadin gwiwar dakarun kasar Syria, da ma sauran mayakan sa kai bayan dauki ba dadi tsawon makwanni. Rahotanni sun ce an kwace birnin ne ta bangaren arewa maso gabashin birnin Aleppo.
Yanzu haka dai dakarun da suka kwace birnin na ci gaba da sintiri, domin kwashe tarin ababen fashewa da mayakan na IS suka bari a cikin sa.
A daya bangaren kuma, kungiyar IS ta bayyana ficewar ta daga birnin nan Al-Bab. Kafin hakan dai IS ta ce sai da ta hallaka mayakan Turkiyya da masu goya masu baya har mutum 400.(Saminu Alhassan)