A zantawarsa da wani gidan talabijin a birnin Astana, Mista Vershinin ya ce, ayyukan rukunin sun hada da, sa ido kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta Siriya, da gudanar da bincika ko gwamnatin Siriya da dakarun da ba sa ga-maciji da gwamnatin suna sabawa yarjejeniyar ko a'a. Ya ce, makasudin kafa wannan rukuni shi ne, kokarin samar da amincewa tsakanin gwamnatin Siriya da dakarun da ke adawa da ita, da kuma ciyar da shawarwarin zuwa gaba. Mista Vershinin ya kara da cewa, kafa wannan rukuni zai taka muhimmiyar rawa wajen farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar Siriya da yankunan dake kewaye da ita.(Murtala Zhang)