Mr. Roach ya ce tattalin arzikin Sin ya bunkasa da kaso 6.7 bisa dari a shekarar 2016, kamar yadda gwamnatin kasar ta tsara, kaza lika zai kai kaso 1.2 na jimillar mizanin GDP na duniya baki daya a shekarar nan da muke ciki.
Kaza lika Roach ya ce duk da hasashen da bankin bada lamuni na duniya IMF ya yi, na bunkasar tattalin arzikin duniya kan kaso 3.1 bisa dari a bana, Sin ce kasa daya tilo da za ta samar da kaso 39 bisa dari, na daukacin ci gaban tattalin arzikin duniya. Wanda hakan ya haura na sauran kasashen duniya baki daya. (Saminu)