A yayin taron, Mr.Xie, ya bayyana cewa, ko da yake cikin rabin shekara da ta gabata, an gamu da kalubaloli da dama kan batun Syria, amma kasar Sin ta ci gaba da dukufa wajen ciyar da shawarwarin dake tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa gaba, da kuma warware matsalar ta hanyar siyasa. Haka kuma, a halin yanzu, kasar Sin ta yi imanin cewa, za a iya warware matsalar Syria ta hanyar siyasa, shi ya sa za ta ci gaba da ba da gudummawa kan wannan batu, yayin da kuma yin hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa wajen warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa.
Baya ga haka, Xie Xiaoyan, ya jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa da kuma yin shawarwarin neman sulhu a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, sabo da ba za a iya warware matsalar ta hanyar daukar matakan soja ba, kuma ya kamata a mai da hankali kan ayyukan tsagaita bude wuta, yunkurin siyasa, samar da taimakon jin kai da kuma yaki da ta'addanci a yayin da ake ciyar da wannan aiki gaba.
Haka kuma, kasar Sin tana ci gaba da ba da taimako kan sassauta matsalar jin kai a kasar Syria, ta bukaci gamayyar kasa da kasa da su kara ba da taimakon jin kai ga kasar Syria karkashin kwamitin tsaron MDD, har ma ta samar wa kasar taimako cikin himma da kwazo. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samarwa kasar Syria da wasu kasashen dake kewayenta taimakon kayayyaki da adadinsu ya kai dallar Amurka miliyan 480, sa'an nan, ta kuma baiwa kungiyar Red Cross da hukumar 'yan gudun hijira ta MDD taimako kudade a lokuta da dama. A halin yanzu, kasar Sin ta dukufa wajen cimma alkawarinta na samar da taimakon kudi na RMB miliyan 230 da kuma taimakon abinci na ton dubu 10. (Maryam)