in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na nuna damuwa matuka game da tsanantar halin tsaro a Syria
2016-10-10 19:52:08 cri

Yau Litinin 10 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta nuna damuwa sosai game da tsanantar yanayin tsaro a kasar Syria, tana kuma fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki, musamman ma kasashen da suka fi yin tasiri kan batun Syria, za su mayar da batun wanzar da zaman lafiya a duniya, da kuma tsaron lafiyar al'ummar Syria a gaban komai.

Kaza lika Sin na fatan sassan za su kuma ci gaba da kara azama wajen warware batun kasar ta Syria a siyasance. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China