Jiya Talata 21 ga wata, rundunar sojin kasar Sudan da masu adawa da gwamnatin kasar, sun dorawa juna laifin sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da ta hargitsi a jihar Kordofan ta Kudu.
Tun a shekarar 2011 ne Rundunar sojan kasar Sudan ta fara yakar masu adawa da gwamnati wato kungiyar 'yantar da jama'ar Sudan (SPLM).
A watan Yunin 2016 ne, shugaban kasar Omer Hassan Ahmed Al-Bashir ya sanar da tsagaita bude wuta na tsawon watanni 4, inda daga baya kuma, ya yi ta tsawaita wa'adin tsagaita bude wutan.
A ranar 15 ga watan Janairun bana ne gwamnatin kasar Sudan ta tsayar da kudurin ci gaba da tsagaita bude wuta na tsawon watanni 6 a dukkan wuraren kasar da rikici ya shafa. (Tasallah Yuan)