Rahoton ya kuma bayyana cewa, kashi 65 cikin dari na 'yan gudun hijirar yara ne, kuma da yawa daga cikinsu suna fama da matsananciyar yunwa.
Dangane da haka ne, hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD ta shirya samar musu kayayyakin da suke bukata, ta yadda za a ba su taimako cikin gaggawa.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa, za a iya samun karin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da za su nemi mafaka a kasar Sudan. (Maryam)