Wannan yarjejeniyar wacce aka cimma a Juba a Jumma'ar da ta gabata, za ta baiwa kwararru a fannin kiwon lafiya daga kasar Sin damar bude cibiyoyin gwaje gwaje da na gudanarwa a kasar ta gabashin Afrika.
An cimma wannan yarjejeniyar ce a yayin wata ganawa tskanin manyan jami'an gwamnatin Sudan ta kudu da kuma tawagar kwararrun kiwon lafiya 15 na kasar Sin, wadda ke karkashin shugabantar Wang Yuming, wani babban jami'in hukumar kiwon lafiya da tsara iyali ta lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.
Ministan kiwon lafiya na Sudan ta kudu Riek Gai Kok, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan yarjejeniyar wani bangare ne daga cikin tallafin dala miliyan 33 wanda gwamnatin Sin ta alkawartawa sashen lafiya na Sudan ta kudu. (Ahmad Fagam)