in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta bayyana rashin jin dadinta kan shawarar Trump na hana 'yan kasar shiga Amurka
2017-01-29 12:43:17 cri
Gwamnatin Sudan ta bayyana takaicinta dangane da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na hana 'yan kasarta shiga kasar ta Amurka

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta rabawa manema labarai, ta bayyana cewa, matakin Amurkar na zuwa ne bayan da kasashen biyu suka fara tattaunawa game da yadda za su yi mafani da albarkatun kasa, jama'a da tattalin arzikin da Allah ya hore musu wajen zuba jari da raya harkokin kasuwanci, ta yadda zai amfanawa al'ummomin kasashen biyu.

Bugu da kari,mahukuntan na Sudan sun jaddada kudurinsu na hada kai tare da bangaren Amurka a fannin yaki da ta'addanci. Kasar Sudan ta kuma yi kira ga Amurkar da ta hanzarta cire sunan kasar daga jerin kasashen da Amurka ta ayyana a matsayin kasashen da ke taimakawa 'yan ta'adda.

A ranar 13 ga wannan wata ne tsohon shugabna Amurka Barack Obama ya sanya hannu kan wasu umarnin shugaba guda biyu, da nufin soke takunkumin tattalin arziki da Amurkar ta kakabawa kasar Sudan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China