in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin kasa da kasa sun yi kira da a kawo karshen dauki ba dadi a Sudan ta kudu
2017-01-30 12:25:35 cri
Wakilan MDD da na kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU, tare da na kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, sun fidda wata sanarwar hadin gwiwa, wadda ke kira da a gaggauta dakatar da musayar wuta a Sudan ta Kudu.

Sanarwar da sassan suka fitar bayan taron su na ranar Lahadi, ta bayyana matukar takaici, game da yadda tashe tashen hankula ke kara yaduwa a sassan kasar, wanda hakan ke iya fadada zama doya da man ja tsakanin kabilun kasar, tare da ta'azzara yanayin jin kai tsakanin fararen hula.

Sanarwar wadda aka fitar a birnin Juba, a yayin da taron shugabannin kungiyar AU na birnin Addis Ababan kasar Habasha ke gudana, ta kara da cewa, sassan za su ci gaba da hadin gwiwa, domin lalubo hanyoyin wanzar da tsaro, da zaman lafiya, da daidaito a kasar.

Sudan ta Kudu dai ta tsunduma cikin matsalolin tsaro ne tun cikin shekara ta 2013, lokacin da dambarwar siyasa ta barke, tsakanin shugaban kasar mai ci Salva Kiir, da korarren mataimakin sa Riek Machar.

Rahotanni na cewa tashe tashen hankula da ake fama da su a kasar sun kai matsayin koli, idan aka danganta da wadanda wasu kasashen duniya ke fama da su, lamarin da ya sabbaba kisan fararen hula masu yawa, tare da raba miliyoyin al'ummar kasar da gidajen su.

Hukumomin kasa da kasa dai na cewa babu wata hanya ta warware rikicin siyasar kasar, wadda ta wuce hawa teburin shawara, musamman ta hanyar amfani da tanajin yarjejeniyar ARCSS da aka cimma a shekarar 2015. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China