A cewar masanan Afirka, wannan manufar da kasar Sin take sa ran za a gudanar da ita, ta dace da bunkasuwar kasashen Afirka, har ma da duk duniya baki daya.
Shehun malami a jami'ar Addis Ababa ta kasar Habasha Konstantinos ya bayyana cewa, bunkasuwar kasashen Afirka baki daya na bukatar kasashen duniya su shiga a dama da su a harkokin zaman lafiya da yin gasa cikin adalci. Tunanin kasar Sin ya dace da bukatar kasashen Afirka wajen shiga harkokin bunkasuwar kasa da kasa a nan gaba.
Bugu da kari, shehun malamin ya ce, a halin yanzu, kasar Sin tana aiwatar da manufar gina makomar bil Adama cikin hadin gwiwa yadda ya kamata, kuma, ana mai da hankali kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Kana, ko shakka babu, taimakon da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka game da gina ababen more rayuwa, zai warware matsalolin da suke hana bunkasuwar kasashen Afirka. (Maryam)