Kakakin hukumar kula da ayyukan gaggawa na birnin Pretoria John Bidesai ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa hadarin ya haddasa jikkatar mutane tsakanin 100 zuwa 150, kuma 20 daga cikinsu na dauke da raunuka masu tsanani.
Haka kuma, wani mai aikin ceto na hukumar ba da taimakon jinyar gaggawa dake wurin, ya bayyana cewa jiragen biyu sun yi karo ne a kan hanyar jirgin kasa guda daya, sai dai ba a kai ga tantance dalilin da ya haddasa aukuwar hakan ba, kuma ba a san dalilin da ya sanya suka hau layin dogo daya ba.
Hadarin dai ya auku ne a lokacin da mutane ke da matukar yawa a jiragen kasa, kuma a lokacin, an yi ruwan sama a birnin na Pretoria. (Maryam)