in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da jagorantar ci gaban sashen yawon bude ido a Afirka ta kudu
2017-02-21 09:40:39 cri
Wasu alkaluman kididdiga da aka fitar a jiya Litinin, sun nuna cewa kasar Sin ce ke kan gaba, wajen bunkasa harkar yawon bude ido a Afirka ta kudu, inda kididdiga ta nuna cewa, Sinawa da suka ziyarci kasar a bara sun karu da kaso 38 bisa dari.

Hakan a cewar ministan ma'aikatar yawon bude ido na Afirka ta kudu Derek Hanekom, ya biyo bayan saukaka matakan samar da Visa ne da aka yi ga baki masu ziyartar kasar. Mr. Hanekom ya kara da cewa, kasar sa na da damar bunkasa wannan harka, ta yadda karin Sinawa, da ma baki daga sauran kasashen duniya, za su rika shiga Afirka ta kudu domin bude ido.

A bara dai Birtaniya ce ke kan gaba wajen yawan 'yan yawon shakatawa da suka shiga kasar, sai kuma 'yan kasashen Amurka da kuma Jamusawa.

Wasu alkaluman kididdiga sun nuna cewa, harkar yawon bude ido ta samarwa Afirka ta kudu kudaden da yawan su ya haura dala miliyan 10, adadin da ya haura na shekarar 2015 da kusan kaso 13 bisa dari.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China