An dai bude taron wanda aka yiwa lakabi da "Energy Indaba" ne a jiya Litinin, kuma mahalartan sa za su maida hankali sosai, ga zakulo hanyoyin cin moriyar nau'o'in makamashi da kasashen nahiyar ke da su. Wannan taro dai na yini 3 na samu halartar wakilan gwamnatoci, da 'yan kasuwa tare da masu zuba jari.
Da ya ke gabatar da jawabi a yayin bude taron, mataimakin babban darakta, kuma shugaban sashen sarrafa iskar gas na Afirka ta kudu Dr. Garth Strachan, ya ce albarkatun iskar gas da aka gano a kasashen Mozambique, da Angola da kuma Tanzania, za su bada damar samar da karin makamashi a Afirka.
Har wa yau Dr. Strachan ya ce akwai bukatar kasashen nahiyar su hada kai da juna, wajen cin gajiyar fa'idojin dake tattare da makamashin iskar gas. Ya ce sashen na kunshe da damammaki na samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arzikin daukacin nahiyar ta Afirka.(Saminu Alhassan)