in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu: An yi kira da a baiwa 'yan Najeriya kariya
2017-02-21 09:30:15 cri
Mahukuntan Najeriya sun yi kira ga takwarorin su na Afirka ta kudu, da su hanzarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na kare 'yan Najeriya, da ma sauran baki daga kasashen Afirka dake zaune a kasar.

Da take jaddada wannan kira cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mataimakiya ta musamman ga shugaban Najeriya game da harkokin kasashen waje da 'yan ci rani Abike Dabiri-Erewa, ta ce far wa baki mazauna Afirka ta kudu da ke yawan aukuwa, abu ne da sam bai dace ba.

Kaza lika Abike ta ja hankalin kungiyar hadin kan Afirka ta AU, da ta sa baki game da wannan matsala da baki ke fuskanta a Afirka ta kudu. Daga nan sai ta yi kira ga 'yan Najeriyar dake zaune a kasar, da su yi taka-tsantsan, duba da cewa har yanzu mahukuntan Afirka ta kudu, sun gaza shawo kan wannan matsala ta kyamar baki da ake fama da ita a kasar.

A baya bayan nan ne dai wata kungiyar 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu, karkashin shugabancin Ikechukwu Anyene, ta tabbatar da farmakin da ake kaiwa bakin, tare da wawashe dukiyoyin su a yankin yammacin Pretoria.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China