Masanan sun bayyana hakan ne a yayin taro karo na 5, na tattauna batutuwan da suka shafi fadada harkar sufurin jiragen sama, a birnin Kigali fadar mulkin kasar Rwanda. Wannan bukata dai za ta kasance muhimmiya, idan aka yi la'akari da karuwar bukatar sufurin sama, da kuma dakon hajoji da ake yi tsakanin nahiyar da sauran sassan duniya, kamar dai yadda masanan suka bayyana.
Cikin jawabin sa yayin bikin bude zaman, babban manajan kamfanin dake bada shawarwari game da filayen jiragen sama dake birnin Vienna, Mr. Johann Frank, cewa ya yi yadda hankula ke kara karkata ga harkokin zuba jari a nahiyar Afirka, da fadadar harkokin yawon bude ido, da shigar kamfanonin kasashen ketare wannan nahiya, ya kara karfafa bukatar inganta kayayyakin aiki a filayen jiragen saman dake nahiyar ta Afirka.
Daga nan sai ya sabunta kira ga kasashen nahiyar, game da bukatar da ake da ita, ta inganta gine gine, da samar da kayan aiki, tare da na lura da ka'idoji zirga zirgar jiragen sama a daukacin sassan nahiyar.(Saminu Alhassan)