in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shiru don nuna alhinin rasuwar zaunannen wakilin Rasha dake MDD
2017-02-21 10:42:55 cri

A jiya Litinin 20 ga watan nan ne zaunannen wakilin kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya rasu a hedkwatar MDD dake birnin New York. A wannan rana, an yi shiru na minti daya domin nuna juyayi kan rasuwar Mr. Churkin, kafin kuma a gudanar da cikakken zaman taron MDD karo na 71.

Rahotanni sun bayyana cewa a jiya Litinin, zaunanniyar tawagar wakilan kasar Rasha dake MDD ta shaida cewa Mr. Churkin ya rasu ne a yayin da yake aiki a ofishinsa, a kuma gabar da ake shirin taya shi murnar cika shekaru 65 a yau Talata, sai dai kuma ba a fidda karin bayani kan dalilin rasuwar sa ba.

A jiyan ne aka kira cikakken zaman taron na MDD karo na 71, a helkwatar MDD dake birnin New York, inda aka saurari rahoto game da raya tawagar ayyukan musamman ta MDD. Shugabar tawagar, kana zaunanniyar wakiliyar kasar Saudiyya dake majalissar Lana Zaki Nusseibeh, ta sanar da labarin rasuwar Mr. Churkin ga mahalarta taron, sa'an nan ta nuna juyayi ga gwamnatin kasar Rasha, da tawagar wakilan kasar, da kuma iyalan Mr. Churkin.

Shugaban babban taron MDD karo na 71 Peter Thomsen, ya ce ya kadu matuka da gaske game da rasuwar Mr. Churkin, kuma tabbas za a yi ban kwana da wannan babban jarumi na kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China