A yayin zaman kwamitin raya cigaba na MDDr karo na 55, tuni kwamitin MDD ya cimma matsaya kan wannan shirin, sannan ya yi kira ga shirin raya cigaban da ya ba da fifiko ga ci gaban tattalin arzikin da zamantakewa a nahiyar Afrika.
A shekarar 2012 ne kasar Sin ta bullo da wannan shirin, da ma dai shiri ne dake da muradin bunkasa cigaban gwamnatoci na kasashen duniya, inda ya tanadi muhimman hanyoyi da kuma matakai da za su tabbatar da ingiza ci gaban duniya baki daya.
Jami'in diplomasiyyar ya ce, wannan shi ne karon farko da taron MDDr ya amince da wannan kuduri wanda kasar Sin ce ta bullo da shi.
Wannan mataki ya nuna a fili yadda mambobin MDD suka amince da wannan shiri na kasar Sin, wanda Sin ta daura aniyar tallafawa ci gaban gwamnatoci na kasashen duniya. (Ahmad Fagam)