Kwamitin sulhun ya yi muhawara a fili game da tabbatar da tsaron ayyukan more rayuwa a wannan rana tare da zartas da kudurin, inda kwamitin sulhun ya kalubalanci kasa da kasa da su tsara manufofin rage hadarin da ake kawowa ayyukan more rayuwa yayin da harin ta'addanci ya faru, kana za a gurfanar da wadanda suke kaddamar da harin ta'addancin kan kayayyakin more rayuwa a gaban kotu.
Kudurin ya bayyana cewa, kwamitin sulhun na MDDr ya kalubalanci kasa da kasa da su yi mu'amala da juna da yin hadin gwiwa a fannonin magance, da rage yin bincike kan hare-haren ta'addancin da ake kaiwa manyan ayyukan more rayuwa. Kwamitin sulhun ya kalubalanci kasashe masu karfi da su samar da gudummawa ga sauran kasashe a fannonin horas da fasahohi da dai sauransu.
A madadin babban sakataren MDD, daraktar ofishin babban sakataren MDD Maria Luiza Ribeiro Viotti, ta yi jawabi a gun taron inda ta bayyana cewa, ana bukatar kasa da kasa da su hada kai wajen tinkarar ayyukan ta'addancin da aka gudanar a tsakanin kasa da kasa. (Zainab)