Yayin wata ganawar sirri wanda shugaban karba-karba na kwamitin sulhu na watan Fabrairu kana jakadan kasar Ukraine a MDD Boloymyr Yelchenko ya jagoranta, baki dayan mambobin kwamitin su 15 sun yi Allah wadai da gwaje-gwajen makamai masu linzami da Koriya ta arewan ta yi a lokutan daban-daban..
Jakada Boloymyr ya shaidawa manema labarai bayan ganawar cewa, kasar Koriya ta Arewa tana kokarin mallakar makaman kare dangi tare kuma da kara zaman zullumi a yankin.
shi ma babban sakataren MDD Antonji Gutterres ya yi Allah wadai da gwajin makami mai linzami na baya-bayan da kasar Koriyar ta yi, yana mai bayyana matakin a matsayin kara keta kudurin kwamitin sulhu.
Guterres ya bayyana cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa cewa, wajibi ne Koriya ta Arewa ta martaba dukkan dokoki kasa da kasa kana ta dakatar da shirinta na kera makaman nukliiya.(Ibrahim)