in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya nemi sanya jami'in kasar Faransa a matsayin mataimakinsa mai kula da shirin wanzar da zaman lafiya
2017-02-15 15:36:02 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya sanar da niyyarsa ta nada wakilin Faransa Jean Piere Lacroix a matsayin Mataimakin Sakataren Majalisar mai kula da shirin wanzar da zaman lafiya.

Lacroix mai shekaru 56, zai fara aiki kan sabon mukaminasa ne a ranar 1 ga watan Afrilun bana, bayan magabancinsa Herve Ladsous, da ya shafe shekaru shida kan mukamin ya sauka.

A yanzu dai, Lacroix shi ne Daraktan MDD da hukumomin kasashen waje a ma'aikatar harkokin wajen Faransa.

Cikin wata sanarwa, Guterres ya kuma sanar da cewa, Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman, zai ci gaba da kasancewa kan mukaminsa na tsawon shekara guda, har sai ranar 1 ga watan Afrilun badi.

Feltman dake wakiltar Amurka, ya kasance kan mukamin tun a shekarar 2012. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China