in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a kasar ta Pakistan
2017-02-17 10:52:57 cri
Babban sakataren MDD Antonoio Guterres ya bayar da sanarwa a jiya ta hanyar kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a kasar ta Pakistan. Sannan ya kalubalanci mahukuntan kasar da su hanzarta kama masu hannu a wannan hari.

Ya kuma jajantawa gwamnatin kasar Pakistan da jama'arta gami da iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon harin. Ya ce, MDD tana goyon bayan matakan gwamnatin kasar Pakistan na yaki da ta'addanci bisa tushen girmama ka'idojin kasa da kasa da na hakkin dan Adam. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China