in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kiran da a daina alakanta ayyukan ta'addanci da addinin Islama
2017-02-13 09:59:10 cri
Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kiran ga kasashn duniya da su yaki masu kokarin alakanta ayyukan ta'addanci da addinin Islama.

Mr Guterres wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da sarki Salman bin Abdullaziz na Saudiya, ya kuma jaddada muhimmancin rawar da hadin gwiwar da MDD da Saudiya ke takawa a yakin da ake yi da ayyukan ta'adanci a sassa daban-daban na duniya.

Babban sakataren na MDD ya kuma yabawa mahakuntan kasar Saudiya dangane da taimakon da suka baiwa tawagar 'yan adawar Syria a tattaunawar zaman lafiyar da aka gudanar a birnin Geneva.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Saudiya Adel bin Ahmed Al-Jubeir ya bayyana cewa, a yayin wannan ziyara shi da sakataren na MDD sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen Syria, Libya da kuma yadda za a yaki ayyukan ta'addanci.

Minista Adel ya kuma kara tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasarsa da kasar Amurka, yana mai cewa, sassan biyu sun amince kan fannoni da dama.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da babban sakataren MDD ya kai kasar Saudiya tun hawansa wannan mukami, Inda sarki salman na Saudiya ya taya shi murnar zama babban sakataren MDD tare da yi masa fatan alheri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China