in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burkina Faso: za a bude dandalin ICT
2017-02-21 10:30:09 cri

Kasar Burkina Faso za ta shirya taron dandalin tattaunawa kan fasahar bayanai da aikin sadarwa na nahiyar Afirka a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar a watan Yunin bana.

Babban taken taron da za a gudanar daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Yuni shi ne, amfani da fasahohin zamani don sauya hanyar bukasar tattalin arziki. Taron dai wani bangare ne na makon kasar, dangane da harkokin yanar gizo ta Internet, da fasahar bayanai da aikin sadarwa, wanda zai gudana daga ranar 20 zuwa 25 ga watan na Yuni.

Fasahar sarrafa bayanai dai a yanzu haka na samar da boyayyen karfi na samar da ci gaba, kana tana taimaka sosai wajen yin takara, da bukasa fannin kirkire-kirkire, da bunkasar tattalin arziki ba tare da kasala ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China