PNDES wani muhimmin shiri ne da zai iya kai kasar Burkina Faso ga kasancewa kasa mai tasowa sosai, in ji mista Ngom, bayan wata ganawa tare da shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré.
Shugaba Kabore an zabe shi ne bisa tushen shirin PNDES, wato sabon ma'aunin bunkasuwa na Burkina Faso kan wata bunkasuwar da ta kashi 7.3 cikin 100 bisa lokacin shekarar 2016 zuwa shekarar 2020 da kuma samar da guraben ayyukan yi dubu 50 a kowa ce shekara.
Ranakun 7 zuwa 8 ga watan Disamba, Burkina Faso za ta shirya a birnin Paris na kasar Faransa da wani dandalin kan zuba kudin PNDES tare da abokan huldar kudi da fasaha, domin kokarin tattara kudin Sefa biliyan 8.6 da suka rage wajen gudanar da shirin PNDES. (Maman Ada)