in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faraministan Burkina Faso ya nemi bankin duniya da ya zuba kudi domin wani babban shirin cigaba
2016-10-04 12:46:23 cri
Faraministan kasar Burkina Faso Paul Kaba Thieba na ziyarar aiki tun daga ranar uku zuwa bakwai ga watan Oktoba a birnin Washington na kasar Amurka, inda zai gana da shugaban bankin duniya, domin tattauna batun zuba kudi ga shirin kasa na cigaban tattalin arziki da jama'a (PNDES).

A cewar wata sanarwa ta fadar faraminista, shugaban gwamnatin Burkina Faso, kuma zai halarci wani taron aiki tare da kwararrun bankin duniya, dake kula da shirin shirya wani zaman taron masu bada lamuni a cikin watan Disamba mai zuwa a birnin Paris, kan zuba kudi ga shirin PNDES.

Haka zalika, mista Thieba zai gana tare da darektar asusun IMF, madam Christine Lagarde, da sauran shugabannin duniya masu ruwa da tsaki a fannin kudi, da kuma manyan 'yan kasuwan Amurka.

PNDES, wani sabon shirin cigaba ne na Burkina Faso bisa tsawon lokacin shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, da aka tsara bisa tushen halartar kowa da kuma yin nazari sosai kan matsalar kasa.

Haka kuma, yada nufin karya tsarin shingaye ga duk wani ci gaba ta yadda za a kai ga wata bunkasuwa mai karfi, karko kuma ta kowane fanni, in ji wannan sanarwa dake kuma jaddada cewa aiwatar da shi na bukatar tattara kudade fiye da Sefa biliyan 15 wadanda kuma kashi 63.8 cikin 100 zai fito daga aljihun gwamnati kana kashi 36.2 daga kungiyoyi masu bada lamuni, bangaren masu zaman kansu na gida dana waje, da kuma 'yan Burkina Faso dake zaune a ketare. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China