Rahotanni na cewa, kimanin wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba a tantance su guda 40 ne suka kai hari a kan sansanin sojojin na Nassoumbou, inda suka hallaka sojoji 12.
A cikin wata sanarwar da jam'iyyar MPP ta rabawa manema labarai a ranar Asabar, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan abin da kira harin dabbaci da aka kai, kana ta jinjinawa sojojin da aka kashe a yayin da suke kokarin kare martabar kasarsu.
Bugu da kari, jam'iyyar ta yi Allah-wadai da matakan 'yan ta'addan na kokarin jefa kasar cikin tashin hankali. A don haka ta bukaci gwamnati da ta kara sanya ido don gudun aukuwar irin wadannan hare-hare a nan gaba.
Kasar Burkian-Faso dai ta fuskanci tashe-tashen hankulan a wannan shekara da ke shirin karewa ta 2016, inda a watan Janairu wasu 'yan bindiga suka kaddamar da munanan hare-hare a dakin cin abincin Cappuccino da otel din Splendid a Ouagadougou, babban birnin kasar, hare-haren da suka yi sanadiyar rayukan mutane 30. (Ibrahim)