in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burkina Faso ta samu Tallafin dalar Amurka miliyan dari daga Bankin Duniya domin bunskasa Lantarki
2016-12-23 10:52:52 cri
Wata sanarwa da aka fitar jiya a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso ta ce, Bankin Duniya ya ware dala miliyan dari domin samar da lantarki da sake fasalin tara haraji a kasar.

Ministan kudi da kula da tattalin arziki na kasar, Rosine Coulibaly da Manajan Bankin Duniya da ke kasar ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Laraba a Ouagadougou.

A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin kudin kasar ta fitar, ana sa ran kudin da ya kunshi rancen dala miliyan hamsin da biyar da tallafin dala miliyan arba'in da biyar, zai taimakawa kasar wajen bunkasa bangarorinta na lantarki da hada-hadar kudi.,

Ministan Lantarki da ma'adanai na kasar Alpha Omar Dissa, ya ce tallafin ya zo a lokacin da ya dace, a daidai lokacin da gwamnati ta dauki batun bunkasa lantarki da baza komar tattalin arziki a matsayin muhimman batutuwa.

Har ila yau, Sanarwar ta ruwaito cewa, za a sanya wani bangare na kudin wajen kara bunkasa samar da lantarki, ta hanyar samar da tashar lanatarki mai amfani da hasken rana, mai mega watt talatin.(Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China