A gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, Simon Compaore ya ce, kimanin dakarun tsohon shugaban kasar 30 ne suka kai hari a fadar shugaban kasar mai ci, da kuma sansanin soja dake birnin Ouagadougou, babban birnin kasar.
Ban da wannan kuma, sun yi yunkurin kubutar da tsohon ministan harkokin wajen kasar Janar Gilbert Diendere, da kuma kwamandan tsohuwar rundunar tsaron shugaban kasar Djibril Bassole, da ake tsare da su a wani gidan yari na soja, a wani yunkuri na kifar da shugaba mai ci a yanzu Christian Kabore .
A cewar 'yan sandan, an gano wasu mutanen da ake zarginsu da hannu a wannan lamari a ranar 8 ga wannan wata a kan hanyarsu ta zuwa Ouagadougou, kuma an harbe biyu daga cikinsu har lahira, sannan wani dan sanda guda ya ji rauni.
Ministan tsaron kasar Burkina Fason ya ce, yanzu haka an kama wasu sojoji 19 da ake zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin sojan da bai samu nasara ba. (Lubabatu)