in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a soke takunkumin da aka sanya wa Sudan
2017-01-18 19:23:48 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin ba ta goyon bayan sanya wa wata kasa takunkumi bisa radin kai, don haka take kira da a soke takunkumin da aka kakabawa kasar Sudan ba tare da wani bata lokaci ba.

A kwanakin baya ne dai shugaba Obama na kasar Amurka, ya ce kasarsa na fatan sassanta takunkumin da ta sanya wa kasar Sudan. Don gane da hakan, Madam Hua ta ce, kasar Sin ta lura da niyyar Amurka, kuma tana maraba da hakan. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China