in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban babban bankin Sudan ta kudu zai magance hawa-hawar farashi a kasar
2017-01-18 10:37:24 cri
Sabon shugaban babban bankin Sudan ta kudu Othom Rago Ajak, ya fada a jiya Talata cewa, zai bada fifiko wajen daukar matakan dakile hawa-hawar farashin kayayyaki, lamarin da ke gurgunta ci gaban tattalin arzikin kasar mai fama da yake yake.

Ajak ya ce, babban abin da ke ci wa kasar tuwo a kwarya shi ne, tashin farashin kayayyaki, da rashin daidaita kayyadadden farashi a kasuwannin musayar kudade a kasar. Ya ce za su ci gaba da aiki tukuru domin shawo kan wadannan matsaloli, kuma suna da kyakkyawar fatar samun nasara.

Bayan da yaki ya kara rincabewa a kasar ta Sudan ta kudu, an samu mummunan tsadar kayayyaki a kasar wanda ya kai kashi 835.7 cikin dari zuwa karshen watan Oktoba, lamarin da ke kara karyewar darajar kudin kasar (SSP) idan aka kwatanta da dalar Amurka, kuma lamarin ya haifar da tsadar kayayyakin masarufi.

Tashin hankalin da ya barke shekaru sama da uku da suka gabata a kasar mai arzikin man fetur, kana da matsalar faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, ya haifar da mummunan gibi game da man fetur da kasar ke samarwa a yankin arewacin kasar mai arzikin mai dake tekun Nile na jahar Unity, sun haifar da koma baya ga kasar wajen samun kashi 98 cikin 100 na kudaden shigar da za ta yi amfani da su a kasafin kudinta na shekara.

A watan Yunin shekarar da ta gabata, asusun ba da lamuni na IMF, ya gargadi Sudan ta kudu da ta rage hanyoyin kashe kudinta marasa amfani, kana ta kara fadada hanyoyin samun kudaden shigarta wadanda ba su shafi mai ba, domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.

Sai dai masu nazarin al'amurra na ganin cewa makudan kudaden da kasar ke kashewa wajen sayo makamai don baiwa sojojin kasar a yakin da ake fafatawa a kasar, na daga cikin manyan hanyoyin dake durkusar da kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China