Ana dai fatan kudurin tsagaita bude wutar da takardar bayan taron ta kunsa, zai sanya dan-ba, na kawo karshen dauki ba dadin da bangarorin kasar ta Syria suka shafe kusan shekaru 6 suna gwabzawa.
Kasashen Turkiyya, da Rasha da Iran ne suka dauki nauyin shirya taron na yini biyu. Wakilan su kuma sun gabatar da jawabin bayan taro na hadin gwiwa, suna masu jaddada muhimmancin kare kima da ikon mulkin kai, da yankunan kasar ta Syria. Kaza lika sun amince da cewa daukar ko wane irin mataki na soja, ba zai haifar da kyakkyawan sakamakon da ake fata ba.
Har wa yau kasashen uku, sun amince su ci gaba da daukar matakan wanzar da zaman lafiya, tare da yakar kungiyoyin 'yan ta'adda dake Syria, kamar IS, da Nusra Front mai alaka da Al-Qaida, kana dole ne a ware wadannan kungiyoyi daga 'yan tawaye masu adawa da gwamnatin Syria.
A daya bangaren kuma, sanarwar ta jaddada goyon bayan ta ga aniyar 'yan tawayen na Syria, game da shiga a dama da su a zagaye na gaba na shawarwarin da za a gudanar nan gaba.
Kasashen uku sun kuma jinjinawa nasarar da taron na Astana ya cimma, musamman ganin yadda ya hada tsagin gwamnatin Syria da na 'yan adawar kasar waje guda aka kuma tattauna.