in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminitan Syria ya yi maraba da dukkan kiran da aka gabatar wajen mayar da zaman lafiya a kasar
2017-01-23 13:53:36 cri
Firaministan kasar Syria Imad Hammis ya bayyana a ranar 22 ga wata cewa, game da shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Syria da za a gudanar a birnin Astana na kasar Kazakstan a ranar 23 ga wata, gwamnatin kasar Syria tana maraba da dukkan kiran da aka gabatar wajen mayar da zaman lafiya a kasar.

Wakilan gwamnatin kasar Syria da na 'yan adawa na kasar da manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura, da wakilan kasashen masu neman a gudanar da shawarwari wato Rasha, Turkiya, Iran za su halarci shawarwarin. Ban da wannan kuma, jakadan Amurka dake kasar Kazakstan George Kroll shi ma zai halarci shawarwarin a matsayin mai sa ido. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China