in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan motocin shake da kayan agaji sun isa yankin Homs na Syria
2017-02-13 10:06:54 cri
A jiya Lahadi ne wasu manyan motoci guda 41 shake da kayan agaji suka shiga birnin Rastan na tsakaniyar lardin Homs da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa (ICRC) wadda ta bayyana hakan, ta ce kayayyakin sun hada da kayan abinci da na lafiya da barguna, kuma ake saran za su ishi mutane 110,000 da ke wannan birni.

Kungiyar ta ce, an samu nasarar isar da wadannan kayayyaki ne sakamakon hadin gwiwar kungiyar da takwararta ta Larabawan Syria wato SARC da kuma MDD.

Rahotanni na cewa, har yanzu biranen Rastan da Talbiseh suna hannun 'yan tawayen da ke wajen lardin Homs. Haka kuma yawancin kayayyakin more rayuwa da ke birnin Al-Rastan sun lalace sakamakon fadan da ake gwabzawa a yankin, inda masu fafutuka ke kira ga kungiyoyin ba da agaji su taimaka ta hanyar samar da man gas din da za a sakawa babbar cibiyar samar da ruwan sha da ke birnin.

Masu fafutukar dai suna korafin cewa,dakarun gwamnatin sun kwashe shekaru hudu suna rike da birnin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China